Babban sakataren OPEC Sanusi Barkindo ya rasu
July 6, 2022![Generalsekretär der OPEC Mohammad Barkindo](https://static.dw.com/image/62376570_800.webp)
Talla
A sanarwar da shugaban kamfanin man Najeriya NNPC Male Kyari ya fidda da wannan safiyar a shafinsa na Twitter, ya bayyana rasuwar Barkindo a matsayin babban rashi ga iyalansa da ma'aikatan kamfanin NNPC da ma kungiyar OPEC.
Barkindo ya rasu yana da shekaru 63 a duniya, kafin rasuwar sa, marigayin na gab da sauka daga mukaminsa na sakataren OPEC bayan kwashe sama da shekaru shida.
Ana sa ran a gaba a yau ne za a fidda bayanai a game da jana'izarsa.