SiyasaAfirka
Shugaban rundunar ‘yan sandan Kenya ya yi murabus
July 12, 2024Talla
Shugaban rundunar ‘yan sandan Kenya ya yi murabus daga mukaminsa, sakamakon sukar da aka yi masa kan zanga-zangar kin jinin gwamnati da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama, a cewar fadar shugaban kasa, wanda shi ne babban jami'i na baya bayan nan da guguwar zanga-zangar ta yi awon gaba da shi.
Shugaba William Ruto ya amince da murabus din Japhet Koome, babban sufeton 'yan sandan kasar, a cewar wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar.