1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taro kan yankin Darfur dake yammacin Sudan

July 18, 2006

Sakatare janar na MDD Kofi Annan yayi kira ga kasashe masu ba da tallafi da su taimakawa wata rundunar samar da zaman lafiya ta Afirka ga yankin Darfur mai fama da rikici dake yammacin Sudan. A halin da ake ciki KTT da hukumomin ba da agaji sun yi gargadin cewa duk wani jinkiri da za´a yi zai haddasa asarar rayuka masu yawan gaske. Suka ce Darfur na dab da fadawa cikin wani mummunan bala´i. An yi wannan gargadi ne a lokacin da ake fara wani taron kasa da kasa akan rikicin Darfur wanda zai gudana a birnin Brussels. Hukumomin ba da agaji sun yi korafin cewa masu ba da tallafi na yamma na kin agazawa sojojin kungiyar tarayyar Afirka a Darfur, wadanda suka dogara akan taimakon kasashen yamman. Tun watanni biyu da suka wuce aka sanya hannu kan yarjejeniyar samar da zaman lafiya a Darfur amma halin tsaro sai kara tabarbarewa yake yi. Wani labarin da ya iso mana yanzu yana cewa Amirka ta yi alkawarin ba da euro miliyan 92 yayin da kungiyar EU zata ba da euro miliyan 25 ga rundunar ta AU a Darfur.