Babban taro tsakanin Koriya ta kudu da Koriya ta arewa
August 8, 2007Shugaba Roh Moo-Hyun na Koriya ta kudu da kuma shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Il sun shirya ganarwar ce daga ranar 28 zuwa 30 ga watan agusta da muke ciki a birnin Pyongyang,wanda shine karo na biyu tsakaninsu cikin tarihi.
Koriya ta kudu tace Koriya ta arewa ce ta bada shawarar gudanar da wannan taro,wanda koriya ta kudu take ganin yana da muhimmanci ga batun zaman lafiya tsakaninsu.
Sanarwa daga fadar shugaban Koriya ta kudu tace zasu gudanar da tattaunawar karshe ta zaman lafiya,tun dai shekarar 1953 kasashen biyu suke yakin akida bayan wata yarjejeniya ta ajiye makamai amma ba ta zaman lafiya ba.
Ya zuwa yanzu dai kasar Amurka da wasu manyan kasashe sun yi maraba da wannan taro suna masu baiyana fatar zai kai ga kwance damarar yakin koriya ta arewa mai bin akidar kommunisanci.
Taron wanda zai hada da China da Japan da Amurka da kuma Rasha ana fatan zai bada hanyar samarda taimakon makashi ga koriya ta arewa tare da kafa huldodin diplomasiya tsakani.
Kasar Japan wacce keda dadaddiyar dangantaka mai tasuri da koriya ta arewa tace tana son ganin wannan taro na farko cikin shekaru 7 ya samarda zaman lafiya mai dorewa.
Sakataren majalisar zartaswar Japan Yasuhisa Shiozaki yace Japan tana kuma fatar taron zai tabo batun sace yan kasarta da tayi a shekarun 1970 zuwa 1980 da kuma batun nukiliya na koriya ta arewan.
Kasar China kuma daya daga cikin kasashe kalilan kawayen koriya ta arewa tace tana fatar samun sakamako mai maana a wannan taro.
Mai magana da yawun kasar China Liu Jianchao yace a matasayinta na makwabciya kasar China tana goyon bayan inganta dangantaka tsakanin Koriyoyin biyu ta hanyar tattaunawa.
Kasar ta China dai ta sha karabar bakuncin tattaunar kasashe 6 masu tuntubar juna kan batun nukiliya na Koriya ta arewa.
Sai dai kuma martani daga yan adawa na Koriya ta kudu ya sha banban dana kasashen ketare inda yan jamiyar GNP wadanda sukayi watsi da taron cewa wani yunkuri ne na kara goyoyn baya gad an takara da Roh yake marawa baya, sun kona tutar koriya ta arewa tare da zuba tawada kan hotunan Roh da Kim a lokacin wani gangami da sukayi kusa da fadar shugaban kasa.
Duk da haka dai tsohon shugaba Kim Dae Jung wanda shekarau 7 da suka shige ya karbi bakuncin taron farko tsakanin kasashen biyu ya baiyana cewa wannan wani muhimmnin mataki ne na kaiwa ga zaman lafiya a yankin.