1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taron duniya a birnin Paris kan makomar Libiya

September 1, 2011

Tun gabanin taron tarayyar Turai ta ɗage wani kaso na takunkuman da ta sanya wa gwamnatin Gaddafi.

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ke ɗaukar nauyin taro kan makomar LibiyaHoto: picture-alliance/dpa

Jami'ar kula da harkokin wajen EU Catherine Ashton wadda ta ba da sanarwar ɗage takunkuman a birnin Brussels ta ce an janye haramci da aka sanya wa kamfanonin da hukumomin Libiya guda 28, ciki har da bankuna da kamfanonin mai da na isakar gas. A Jamus kaɗai an ƙiyasta cewa kadarorin Libiya dake cikin ƙasar sun kai na Euro miliyan dubu 7.3, a saboda haka ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle yayi kira da a gaggauta sakin waɗannan kuɗaɗe domin taimakawa al'umomin Libiya.

"Libiya ƙasa ce mai ɗinbim arziki da ya wuce misali musamman na makamashi. Saboda haka ya kamata a ɗage wannan takunkumin da aka ɗaro wa gwamnatin Gaddafi, domin taimakawa a fannonin kiwon lafiya da samar da abinci da sake gina wasu ɓangarorin ƙasar da aka lalata."

Sa'o'i ƙalilan gabanin buɗe babban taron duniya kan ƙasar ta Libiya a birnin Paris na ƙasar Faransa, Rasha mai ikon hawa kujerar naƙi a Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da majalisar wucin gadin 'yan tawayen Libiya a matsayin halastacciyar wakiliyar ƙasar.

Shugaban Faransa wanda ya kira taron na Paris a wannan Alhamis, ya jaddada rawar da ƙasarsa da kuma Birtaniya suka taka a matakan sojin da ƙungiyar NATO ta ɗauka kan Libiya.

"A karon farko tun bayan shekarar 1949, NATO ta tafiyar da aiki a matsayin wata ƙungiyar ƙawance wadda ƙasashen Turai guda biyu wato Birtaniya da Faransa suka jagoranta."

Shugaban na Faransa ya jawo hankali cewa tun farko Amirka ba ta yi niyar shiga a dama da ita sosai a Libiya ba.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu