1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taron jam'iyar CPC a Kaduna

March 2, 2011

Jam'iyar adawa ta CPC ta ƙaddamar da babban taron ganganmi na magoya baya a jihar Kaduna yayin da a waje guda Jam'iyun adawar ke fuskantar ƙalubale daga Jam'iyar PDP na hana musu yin rawar gaban hantsi

an takarar shugaban ƙasa na jam'iyar CPC a Najeriya Janar Muhammadu Buhari mai rítayaHoto: AP

Ɗan takaran shugabancin ƙasa ƙarkashin inuwar jam'iyar adawa ta CPC Janar Muhammadu Buhari mai ritaya ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa yau ɗin nan a birnin Kaduna da ke arewacin Najeriya. Wannan gangami ya baiwa jam'iyar damar share fagen kamfe na 'ya'yanta waɗanda ta tsayar a takarar gwamna a jihohi daban daban na ƙasar.

A waje guda kuma gwamantin tarayyar ta Najeriya ta nesanta kanta daga kalaman da mai baiwa shugaban ƙasar Goodluck Jonathan shawara kan al'amuran majalisa Sanata Abba Aji ya yi game da ƙin amincewa da dokar baiwa 'yan jarida damar bayyana ayyukan gwamanti. Kalaman na Abba Aji na ci gaba da haifar da kace na ce a tsakanin mabobin gwamanati da ma talakawan ƙasar.

Idan aka duba a ƙasa ana iya sauraron sautin rahoton wakilin mu a Kaduna Ibrahima Yakubu akan taron jam'iyar CPC da kuma rahoton Wakilin mu na Lagos Mansur Bala Bello akan martanin gwamnati game da furucin Sanata Abba Aji.

Mawallafi: Mouhamad Auwal Balarabe
Edita: Abdullahi Tanko Bala

I