Guterres ya bude babban taron MDD na bana
September 21, 2021
A yayin bude taron Guterres ya nuna damuwa kan rashin daidaiton da ake samu wurin mallakar rigakafin cutar corona a tsakanin kasashen duniya, yana mai siffanta lamarin da cewa ba abu ne da za a amince da shi ba. Guterres ya nuna bacin ransa kan yadda manyan kasashen duniya suka kusan kammalawa yi wa mutanensu rigakafi a yayin da kaso 90 cikin 100 na kasashen Afirka ba suka kai ga mallakar rigakafin ba.
''Duniyar mu ta shiga wani hali, kama daga matsalar sauyin yanayi da fitintinu da kuma cutar corona, gwiwowinmu za su iya yin sanyi amma ba mu saduda ba. Zabi yana gare mu, za mu iya gyarawa ta hanyar samar da fata nagari a tsakaninmu.'' inji Guterres
Shi ma da yake na sa jawabin Shugaban Amurka Joe Biden ya bukaci kasashen duniya su hada hannu don yaki da corona da sauyin yanayi da kuma rigingimun da ke gudana a Habasha da sauran wurare.