Babban taron MDD karo na 72
September 21, 2017Talla
Jawaban da shugabannin kasashen duniya suka gabatar a babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya tabo takaddamar da ake cigaba da yi kan makaman kare dangi da Koriya ta Arewa ke cigaba da yin gwajinsu da kuma matsalar da Musulmi 'yan kabilar Rohingya na kasar Myanmar ke fuskanta inda kasashen duniya da ma Majaliasar Dinkin Duniya ke cewar kisan da ake yi musu daidai ya ke da yunkuri na sharesu daga doron kasa.