1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban zabe a Saliyo

June 24, 2023

'Yan kasar Saliyo na gudanar da babban zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a daidai lokacin da ake kira kan a kawo karshen matsalar tsadar rayuwa a kasar.

Hoto: Saidu BAH/AFP/Getty Images

Kasar da ke yammacin Afirka, har kawo yanzu dai tattalin arzikinta bai gama farfadowa ba tun bayan yakin basasar kasar a tsakanin shekarar 1991 zuwa 2002 da kuma annobar Ebola da kasar ta yi fama da ita bayan shekaru 10.

Kimanin Maza 12 da mace guda ne suka tsaya takarar neman shugaban kasa a zaben, sai dai kuma shugaban kasar Julius Maada Bio da babban abokin hammayarsa Samura Kamara na jam'iyyar APC su ne manyan 'yan takarar zaben.

Manyan 'yan takarar za su fafata a karo na biyu a jere, bayan da Bio na jam'iyyar Sierra Leone People's Party (SLPP) ya kayar da Kamara a zagaye na biyu na zaben shekarar 2018.

Hukumar zaben kasar ta sanar da cewa, kimanin mutane miliyan 3.4 ne suka yi rijistar zabe wanda fiye da kashi 50 daga cikinsu matasa ne 'yan kasar da shekaru 35.