1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jam'iyyar Democratic Alliance ta marawa shugaba Ramaphosa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 14, 2024

To sai dai jam'iyyar MK ta tsohon shugaban kasar Jacob Zuma ta yi barazanar kauracewa zaman majalisar

Hoto: Nic Bothma/REUTERS

Jagoran babbar jam'iyyar adawar kasar Afirka ta Kudu Democratic Alliance wato DA John Steenhuisen, ya sanar a hukumance cewa sun amince da marawa shugaba Cyril Ramaphosa na ANC baya domin ci gaba da jagorantar kasar.

Karin bayani:Cyril Ramaphosa cikin tsaka mai wuya

A Juma'ar nan ce dai sabuwar majalisar dokokin kasar za ta fara zamanta, tare da zabar sabon shugaban kasa, kuma ANC da DA na da rinjayen kafa gwamnatin hadaka.

Karin bayani:Afirka ta Kudu: Da wa ANC za ta yi hadaka?

To sai dai jam'iyyar MK ta tsohon shugaban kasar Jacob Zuma ta yi barazanar kauracewa zaman majalisar, ma'ana 'yan majalisarta 58 ba za su halarci zaman ba, biyo bayan zargin almundahanar zabe da suka yi.