SiyasaTunusiya
Tunisiya: Abir Mussi za ta yi takara
August 3, 2024Talla
Abir Mussi shugabar jam'iyyart PDL ta 'yan jari huja mai ra'ayin tsofin shugabannin kasar Habib Burgiba da Zine Abdine ben Ali na shirin kalubalantar Kai Saied, wanda aka zaba a shekara ta 2019 kafin daga bisani ya yi babakere a kan mulkin. Moussi, mai shekaru 49, tsohuwar 'yar majalisar dokoki an kamata ne a ranar uku ga watan Oktoba shekarar bara. Ana tuhumarta da manyan zarge-zarge da suka hada da na nufin sauya tsarin gwamnati ta hanyar jan hankali jama'a domin bijrewa gwamnatin.