1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu alamun kawo ƙarshen matsaloli a PDP

January 12, 2011

Rikicin na ci gaba da mamaye jam'iyar PDP da ke riƙe da madafun ikon Najeriya a daidai lokacin da ta ke shirin fitar da wanda zai tsaya mata takara a zaɓen shugaban ƙasa.

Shugaba Goodluck Jonathan na daga cikin masu neman tsayawa PDP takara a zaɓe mai zuwaHoto: AP

Aski dai ya zo gaban goshi a jam'iyar ta PDP da ke jan ragamar mulki a tarayyar Najeriya game da fid da gwanin da zai tsaya mata takara a zaɓen shugaban kasa da zai gudana a watan Afrilu mai zuwa. A daidai lokacin da ya rage sa'o'i ƙasa da 24 a gudanar da taron da zai bayar da wannan dama, manyan ɓangarorin jam'iyar ta PDP na fafatawa da juna da nufin zama gwani a taron da zai gudana a birnin Abuja. Ana wata sai kuma ga wata a ranar Laraba wata kotu da ke garin Inugu na kudacin Najeriya ta yanke hukuncin dakatar da shugaban jam'iyar PDP Chief Nkosilezi Nwodu daga muƙaminsa.

A ƙasa za ku iya jin ƙarin bayani a cikin rahotannin da wakilanmu a Abuja Ubale Musa da kuma Uwais Abubakar Idris suka aiko mana.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal