1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu sauyin shugabanci a kasar Gabon

Umaru AliyuSeptember 2, 2016

Zaben shugaban kasa a Gabon da matsalar 'yan Boko Haram a Najeriya da zanga-zangar adawa da shugaba Robert Mugabe a Zimbabuwe sun dauki hankalin jaridun Jamus.

Gabun - Präsident Ali Bongo Ondimba
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Yalcin

Jaridar Neue Zürcher Zeitung misali, ta maida hankalinta ne kan zaben shugaban kasa da aka gudanar a Gabon, inda ta ce: "Tashe-tashen hankula sun zama ruwan dare a kasar tun da shugaba mai ci, Ali Bongo, bisa ta bakin hukumar zaben kasar, ya sake lashe zaben da aka yi. Sai dai kuma, abokin takararsa a zaben Jean Ping da magoya bayansa suna ci gaba da ikirarin cewar su ne suka sami nasarar wannan zabe. Jim kadan bayan sanar da sakamakon wannan zabe ne tashin hankali ya barke a kasar ta Gabon, inda ma aka kone majalisar dokokin kasar. Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce wannan tashin hankali ya tunatar da nasarar da Bongo ya samu karon farko a shekara ta 1999, inda ya gaji mahaifinsa, Omar Bongo, wanda ya rasu, bayan mulkin shekaru 41.

Boko Haram ta yi mummunan rauni

Jaridar Tageszeitung ta tabo matsalar kungiyar Boko Haram a Najeriya, inda ta ce ko da shi ke kungiyar yanzu dai karfinta ya ragu matuka, mayakanta ba su da wani kuzari sosai, amma dimbin mutanen da suka kama suke garkuwa da su, har yanzu ba a san inda suke ba, kamar dai yadda har yanzu babu wanda ya san abin da ke iya zama makomar kungiyar ta Boko Haram.

Jagoran Boko Haram Abubakar ShekauHoto: picture-alliance/AP Photo

Yayin da mutanen da kungiyar take garkuwa da su har yanzu ba a san inda suke ba, ana ci gaba da iza wutar jita-jitar yiwuwar tattaunawa da wannan kungiya bisa ga neman sakin wadanda ake garkuwa da su, a madadin kwamandojinsu da ke tsare a hannun gwamnati. 'Yan matan Chibok wadanda suka shiga kanun labarai tun da aka sace su daga makarantarsu a watan Afrilu na shekara ta 2014 suna daga cikin wadanda kungiyar ta Boko Haram ta ce za ta fadi inda suke idan gwamnati ta saki mayakan nata. Jaridar Tageszeitung ta ambaci Hussaini Abdu, darektan kungiyar Plan International yana cewa Boko Haram yanzu dai an ji mata mummunan rauni, ba ta da karfin da za ta iya kai manyan hare-hare kamar yadda ta saba yi a can baya.

Jam'iyyar ANC ta doshi hanyar rushewa

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi magana ne kan halin siyasa da ake ciki a Afirka ta kudu, inda ta ce gwagwarmayar neman iko tsakanin shugaban kasa, Jacob Zuma da ministansa na kudi yana kawo barazanar hana zaman lafiya a gwamnatin hadin gwiwa ta kasar. Jaridar ta ce da alamu jam'iyyar ANC da ke mulki tana sha'awar ganin ta rushe kanta da kanta. Wannan dai shi ne yadda ake iya bayanin sabanin da ya taso yanzu tsakanin shugaba Jacob Zuma da ministan kudi, Pravin Gordhan. Ba wani dadadden lokaci ba ne tun da jam'iyyar ta ANC ta sha mummunan kaye a zaben kananan hukumomi a Afirka ta Kudun, yanzu kuma sai gashi tana neman rushe kanta da kanta. Sabanin dai ya tashi ne bayan da aka zargi ministan kudin da laifin cin amanar kasa, saboda a zamanin da yake hukumar binciken haraji, ya fara aiwatar da wani bincike da bai yi wa wasu masu mulki dadi ba.

Hoto: Reuters/P.Bulawayo

A karshe, jaridar Süddeutsche Zeitung ta duba kasar Zimbabuwe, inda ta ce jam'iyyu da kungiyoyi na adawa suna kara hade kansu wuri guda domin kalubalantar mulkin Shugaba Robert Mugabe da ya zama dan mulkin kama karya. Sai dai Mugabe, ya nuna alamun yana sane da abin da 'yan adawar suke yi, kamar yadda a kan ce wai kifi na ganinka mai jar koma. Lokacin wani jawabi ta gidan telebijin na Zimbabuwe, Mugabe ya maida martani ga zanga-zangar da ake ta yi , inda ya ce masu zanga-zangar suna zaton irin abubuwan da suka faru na juyin juya hali a kasashen Larabawa suna iya faruwa a kasarmu. Ya ce yana sanar da masu irin wannan ra'ayi cewar ko kadan hakan ba zai faru a Zimbabuwe ba.