Bacin ran kasashe kan harin Birtaniya
March 23, 2017Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da bayyana takaici kan harin majalisar dokokin Birtabiya da wani ya kai a jiya Laraba, tare da yin Allah wadai da lamarin.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta ce Jamus da al'umarta baki daya na tare da Birtaniya a yaki da ayyukan ta'addanci ta ko wane fanni. Haka Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce manufar Jamus guda ce da Birtaniyar a yaki da ta'addancin.
Jami'an ‘yan sandan birnin London sun ce suna da bayanai kan mutumin da ya kai harin a jiya Laraba wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5 tare da jikkatar wasu sama da 40.
Mutumin dai ya kutsa cikin mutane da mota, a kan gadar Westminster inda masu tafiya a kasa suke, kafin daga bisani ya gangara zuwa majalisar dokokin kasar da ke a birnin na London.
Sai dai fa jami'an 'yan sandan ba su bayar da karin bayani kan mutumin da ya kai harin ba.