Badakalar Aso Rock: Satar bayanai ko cin hanci?
July 2, 2026
A wani abun da ke nuna irin ta'azzara ta damfara a Najeriya, gwamnatin kasar na fafutukar wanke sunanta bisa yadda wani da ta kira dan damfara ya kafa hukuma ta gwamnati da ke da da ofishi da ma kasafi na kudi na gwamnati, ko bayan asusun ajiya na bakuna daban daban.
Najeriyar dai ta dauki lokaci tana ikirarin yaki da damfara, kafin sauyin fasali ya zuwa damfara ta harkar mulkin da ke daukar hankali cikin kasar a halin yanzu. Ana kace-na-ce a tsakanin Mr Adeneyi Adeyemi Mathew da ya ce ya biya kudi wajen samun ofis da kuma fadar gwamnatin kasar da ke fadin takardu na jabu ya kai shi aikata laifin.
Karin bayani: Hukumar EFCC ta Najeriya ta ce ta yi nasarori
Jerin tambayoyin amsawa da ke a bakunan 'yan Najeriya a halin yanzu dai daga dukkan alamu na shirin kara tsawo, bayan da fadar gwamnatin kasar ta ayyana Adeniyi Adeyemi Mathew a matsayin shugaban hukumar bogi. Mutumin da ya dauki lokaci yana jagorantar wata hukumar tsomin baki a cikin harkokin wajen kasar da Abujar tace ta bogi ce.
Hukumar kuma da ta yi nasarar bude asusu a babban banki na kasar da ma samun kasafin miliyan dubu da doriya cikin kudin Najeriyar a shekarar bana, dama uwa uba ofishin harkokinta a rukunin ofisoshin ma'aikatu da hukumomi na gwamnatin kasar da ma daukar aiki ko bayan ganawa da jami'an diplomasiyya na kasa da kasa.
Karin bayani: Zargin EFCC da zama 'yar bi-ta-da-kulli na kara karfi
Duk da cewar dai jami'an tsaro sun yi nasarar kama shi tun cikin watan Oktoban da ya shude, Oga Mathew dai ya ce ya biya babban hafsan mulki na fadar shugaban kasar Naira miliyan dai dai har 400 kafin samun a nada shi kan mukamin nasa. Fadar kuma a fadar Abdul Aziz Abdul Aziz da ke zaman daya a cikin masu magana da yawunta dai ta ce, jami'in ya yi satar sa hannu na hafsan mulkin Femi Gbajabiamilla wajen kaiwa ga samar da takardar nadinsa kan mukamin nasa.
Sakaci a cikin harkar mulki, ko kuma kawar da kai cikin tsarin doka, ana dai kallon badakalar da ta kalli Ogan bogin share tsawon lokaci yana yin hulda da jami'ai na kasashen waje a karkashin inuwar tarayyar Najeriyar dai na iya kara bata suna da kila ma kimar Najeriyar a idanun duniya.
Kasar da har ya zuwa yanzu ke fafutukar wankin suna bisa ayyuka na masu damfara ta yanar gizo, kafin sabon yanayin da ya dauki launin da ke da girman gaske. Duk da cewar dai har ya zuwa yanzu bayanan nisa da kila ma tasiri na damfarar Mathew din basu kai ga bayyana cikin bainar jama'a ba, akalla asusun ajiya 34 da suka hada da wasu guda tara da sun ana hukumar Ogan bogin ke amfani da su kafin kamen nasa.
Karin bayani: Najeriya: Zargin gwamnati da dakile adawa
Kuma tuni damfarar da sunan mulki ya dauki hankali na masu adawa ta kasar da ke fadin a kara bincike, bisa zargin hancin da ya ambato sunan Gbajabiamilan, da kila karyewar tsarin da ya kalli Mathew din cin karensa babu babbaka a hancin fadar mulki ta kasar.
Ko bayan jami'an kasashen waje dai shugaban hukumar bogin ya rika kai ziyara ga ma'aikatu da hukumomi na gwamnatin da suka hada da ita kanta hukumar EFCC mai yaki da kokarin halasta haramun a kasar.