Badakalar cin-hanci a Nijar
October 28, 2013 Yayin wata muhawara da aka shirya a majalisar dokokin kasar ta Nijar, dangane da matakin da gwamnati ta dauka na tsige magajin garin birnin Yamai, a bisa zarginsa da jingina ma'aikatarsa ga wani banki domin karbar bashi. Shugaban majalisar dokokin Malam Hamma Amadou kana shugaban jamiyyar Lumana Afrika, wacce ta fice daga bangaren masu mulki, a sakamakon rikicin da ya biyo bayan kafa gwamnatin hadin kan kasa a Nijar ya bayyana hakan.
Tun dai bayan da shugaban majalisar ya bayyana wanann labari ne batun ya soma haifar da mahawara tsakanin 'yan Nijar. To sai dai lokacin wani taron manema labarai da ya kira don mai da martani, ministan ma'aikatar fasali ta kasa, Malam Cisse Aboubacar ko da ya ke bai karyata batun daukar bashin ba amma ya ce zancen shugaban majalissar dokokin ba gaskiya ba ne.
Ya ce "Jinginar man fetur din kasar Nijar ko kuma mika illahirin kudaden man fetur din da Nijar za ta samu a shekaru uku masu zuwa bai taba tasowa ba. Wannan ba gaskiya ba ne, domin kuwa bashin da mu ka dauka, bashi ne mai sauki da za mu biya a cikin shekaru 25 masu zuwa, dama karin wasu shekaru takwas. Kuma bashin za mu biya shi ne da wani kaso daga cikin kudin cinikin man fetur dinmu, na yankin Agadem da za mu yi. Ba wai jinginar da illahirin kadarar man fetur din namu ba, kamar yadda ake cewa."
Gwamnatin dai ta ce ba ta da niyyar boye wa alu'mma wannan labari, wanda ko ba dade sai ya bi ta hannun majalisar ta bayyana matsayinta a kan bashin, kafin gwamnatin ta samu sukunin amfani da shi. Sai dai kokarin jin martanin bangaran jam'iyar shugaban majalisar dokokin kasar ta Nijar ya ci-tura, inda dukkanin mukarrabansa da aka tuntuba, suka ce a halin yanzu ba za su ce uffan ba, har sai bayan sun nazarci gundarin bayanan da ministan fasalin da ya kare gwamnati ya yi.
Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Usman Shehu Usman