1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Badakalar cinikin jarirai a Nijar

Gazali Abdou TasawaNovember 27, 2014

A Jamhuriyar Nijar matakin kotun daukaka kara ta birnin Yamai na bada belin wasu daga cikin mutanen da ake zargi da hannu a cikin badakalar cinikin jarirai ya janyo ce-ce-kuce.

Hoto: DW/M. Kanta

Matakin kotun dai ya soma haifar da muhawara a tsakanin 'yan kasar musamman ganin mai dakin tsohon shugaban majalisar dokoki Hama Amadu ba ta daga cikin wadanda aka bayar da belin nasu dama kuma yadda matakin ya zo kwana guda da zaben sabon shugaban majalisar dokokin da ya maye gurbin tsohon kakakin da ke zaman gudun hijira a kasar Faransa. Mutane 16 daga cikin wadanda ake zargi da kasancewa da hannu a cikin badakalar cinikin jariran ne dai kotun ta ba da belin su.

Shugaba Mahamadou Issoufou tare da Hama AmadouHoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

Tambayoyi daga magoya baya

Matakin kotun dai ya sanya aza ayar tambaya game da dalilan da ya sanya ta ki sakin mai dakin Hama Amadou, inda wasu 'yan Nijar din musamman magoya bayan Hama ke cewa biri ya so ya yi kama da mutum a game da zargin da ya ke yi na cewa batun cinikin jariran ba komai ba ne illa bita da kullin siyasa da neman shafa masa kashin kaji da gwamnatin Jamhuriya ta Nijar ke yi da nufin hana shi tsayawa takara a zaben shugaban kasa mai zuwa da za a gudanar a shekara ta 2016. To saidai babban alkalin gwamnatin na wanann kotu Ibrahim Boubacar Zakaria ya ce ba wai mai dakin Hama Amadun ce kadai matakin kin bada belin ya shafa ba kana lauyanta bai nemi a bayar da belinta ba.

Maban-ban-tan bayanai daga lauya

To amma lauyan mai dakin Hama Amadun Maitre Soule Umaru ya yi ikrarin cewa ya nemi belin nata kuma ya cika dukkan ka'idojin shari'ar sau da dama ba tare da samun biyan bukata ba a baya. Sanann ya kara da cewa a yanzu haka a shirye ya ke ya sake mika bukatar neman belin mai dakin Hama Amadun. Suma dai daga nasu bangaren wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam na Jamhuriyar ta Nijar sun soma tofa albarkacin bakinsu dangane da wanann hukunci. Yanzu dai 'yan kasa sun zura ido su ga sakamakon da kotun za ta bayar a game da bukatar belin da lauyan mai dakin Hama Amadun zai shigar a gaban kotun dama kuma yanda makomar shari'ar mutanen da aka bayar da belin na su za ta kasance a nan gaba.

Majalisar dokokin Jamhuriyar NijarHoto: DW