1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ministar Jamus tana ziyara a Afirka

Suleiman Babayo ZMA
July 15, 2024

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock tana fara ziyarar aiki a kasashen Senegal da Cote d'Ivoire da ke yankin Afirka ta Yamma a wani matakin karfafaf tsaro da hadin kai.

Jamus Annalena Baerbock
Annalena Baerbock ministar harkokin wajen JamusHoto: dts-Agentur/picture alliance

Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock a wannan Litinin tana fara ziyarar zuwa wasu kasashen yankin yammacin Afirka da suka hada da Senegal da Cote d'Ivoire da nufin karfafa hulda gami da kare ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin Sahel na Afirka.

Karin Haske: Ministar harkokin wajen Jamus za ta kai ziyara yammacin Afirka

Gabanin fara ziyarra ministar ta ce karin samun kasashe karkashin rikice-rikice a yankin zai kara tabarbara lamura kuma tana fata nada shugaban kasar Senegal mai shiga tsakanin kasashen Afira ta Yamma da wadanda suka samu sabani haka zai iya kyautata yanayin da ake ciki. Kasashen na Senegal da Cote d'Ivloire inda ministar harkokin wajen ta Jamus, Baerbock za ta kai ziyara suna cikin kasashen da ke karkashin tsarin mulki na farar hula.