1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka da Houthi na rikici a Bahar Maliya

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 24, 2023

Kakakin kungiyar Houthi Mohammed Abdul-Salam ya ce wani makami mai linzami da jirgin ruwan yakin Amurka ya harba da nufin kai farmaki ga sojojin ruwan Yemen a Tekun Bahar Maliya, ya fashe a kusa da jirgin ruwan Gabon.

Teku | bahar Maliya | amurka | Yemen | Houthi
Jiragen yaki marasa matuka mallakar Amurka a Tekun Bahar MaliyaHoto: Jorge LeBaron/U.S. Navy/abaca/picture alliance

Kakakin kungiyar ta Houthi ta Yemen Mohammed Abdul-Salam ya ce jirgin ruwan dakon kayan mallakar kasar Gabon da makami maai linzamin da Amurkan ta harba ya fashe a kusa da shi, na kan hanyarsa ta zuwa Rasha ne. Ya kara da cewa Tekun Bahar Maliya zai zama tungar yaki, in har Amurka da kawayenta suka ci gaba da cin zarafinsu. A cewarsa tilas kasashen da ke makwabtaka da tekun, su fahimci irin barazanar da hakan ke nufi ga tsaron kasashen nasu. Da ma dai shugaban kungiyar ta Houthi Abdel-Malek al-Houthi ya yi gargadin cewa za su kai hari a kan jiragen ruwan yakin Amurka da ke Tekun Bahar Maliyan, in har Washington ta kai musu hari bayan da ta kafa wata runduna ta musamman ta kasa da kasa domin mayar da martani ga hare-haren 'yan Houthi ga jiragen ruwan dakon kaya a Tekun na Bahar Maliya.