1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Bajamushiya Nahid Taghavi ta samu 'yanci

January 13, 2025

Nahid Taghavi, 'yar Jamus mai asali da Iran ta samu 'yanci bayan hukuncin daurin sama da shekaru 10 da Iran ta yanke mata saboda zargin yada farfaganda kan mahukuntan kasar ta hanyar haramtacciyar kungiya.

 Nahid Taghavi ta shaki iskar 'yanci
Nahid Taghavi ta shaki iskar 'yanciHoto: privat

Bajamushiyar 'yar Iran Nahid Taghavi wadda mahukunkan Tehran suka kama a watan Oktoban 2020 ta shaki iskar 'yanci, kuma tun tuni ta isa Jamus a ranar Lahadi kamar yadda 'yarta da kuma kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International suka sanar.

A cikin wata sanarwa Amnesty International ta ce an saki Nahid Taghavi mai shekaru 70 a duniya bayan ta share kwanaki 1,500 a tsare ba bisa ka'ida ba, kuma ta isa cikin iyalinta lami lafiya.

Da take tsokaci kan batun a shafinta na X, ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta bayyana dowowar matar cikin iyalinta a matsayin babban abin farin ciki bayan shafe shekaru hudu a gidan yari cikin yanayin ukuba.

Sakin Nahid Taghavi na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin tattaunawa kan shirin Iran na nukiliya a kasar Switzerland, mako guda gabanin rantsar da sabon shugaban Amurka Donald Trump.