Baje kolin amfanin gona a Jamhuriyar Nijar
February 12, 2026
Kimanin shekaru 10 kenan da aka soma irin wannan haduwa domin nuna wa 'yan kasar Jamhuriyar Nijar irin fasahar da mata da matasa suke da ita a fannoni da dama na kayayakin da ake sarrafawa a cikin kasar ta Nijar, inda wasu sannu a hankali suke da kayan aiki na sarrafa kayayakin idan aka dubi shekaru da dama da suka gabata.
Dalilin baje kolin
Akasarin matan dai burin da suke da shi, shi ne na sanin irin aikin da suke yi na sarrafa kayayakin da ake iya amfani da su a ko'ina, wanda ta kamata ma'aikatu daban-dabansu rinka oda a wajensu sai dai har yanzu da saura.
Za a ci gaba da nuna wadannan kayayyaki da mata da matasa ke sarrafawa a nan Nijar har ya zuwa ran 15 ga wannan wata tsawon kwanaki hudu kenan. Sai dai ga yadda wannan mata da ke jan kokari kowace daga nata bangare, ya dace a ce sun samu tallafi na kayan aiki ta yadda abubuwan da suke sarrafawa za ishi al'umma ta birnin Yamai da ma ta kasa baki daya har ma su yi tunanin fitarwa waje.