1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNijar

Yamai: Baje-kolin amfanin gona daga Agadez

Salissou Boukari LMJ
January 21, 2026

Duk shekara a daidai wannan lokaci, ake shigar da danyen kaya da manoman yankin arewacin Agadez ke nomawa zuwa Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar.

Nijar | Yamai | 2026 | Baje-koli | Amfanin Gona | Agadez | Manoma
Baje-kolin amfanin gona daga Agadez, a Yamai fadar gwamnatin NijarHoto: Salissou Boukari/DW

Hakan na daga cikin damar da hukumomi Jamhuriyar ta Nijar suka bai wa wadannan manoma, domin su samu damar sayar da kayayyakinsu, duk kuwa da tarin kalubalen da suke fuskanta kafin zuwansu birnin na Yamai. Daman dai a irin wannan lokaci na hunturu ne akasari manoman na yankin Timiya da ke cikin jihar Agadez ke fitar da kayayakin da suke nomawa, wanda kuma aka samar da wannan tsari na baje-kolin kayayyakin da manomansuke nomawa. Duk shekara manoman na kai kayayyakin da suka noma dangin 'ya'yan itace da kayan miya, inda mahakunta da sauran masu fada a ji ke zuwa wurin domin nuna goyon bayansu ga manoman.
Magidanta maza da mata daga ko'ina ne ke kwarara cikin wannan kasuwa musamman ma a lokacin tashi daga aiki ko kuma a karshen mako, inda iyalai ke fita zagaye domin gane wa idanunsu. Sai dai kuma duk da murna da gamsuwa da alumma ke nunawa na samun wadannan kayayyaki da manoman yankin Timiya ke kawowa daga jihar Agadez, a nasu bangare manoman sun ce suna fuskantar gagarumin kalubale kafin su samu isa Yamai, inda kaya da dama ke lalacewa saboda rashin hanya.

Manoma sun sauke farashin abinci a Damagaram

01:39

This browser does not support the video element.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani