1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Baje kolin kayayyakin masana'antu a Jamus

Zainab Mohammed Abubakar RGB
May 31, 2022

An bude kasuwar baje kolin kayayyakin masana'antu na kasa da kasa a birnin Hannover na kasar Jamus. Bikin na bana ya hada kan wakilai daga kasashe dabam-dabam.

Deutschland | Hannover Messe 2022 | Olaf Scholz
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz Hoto: Friso Gentsch/dpa/picture alliance

An bude kasuwar baje kolin kayayyakin masana'antu na kasa da kasa a birnin Hannover. Bikin da zai gudana har zuwa ranar biyu ga watan Junin 2022, ya kuma samu halartar wakilai daga kasashe dabam-dabam na duniya. 

Bikin baje kolin da ke zama mafi girman irinsa ya sake dawowa bayan tsaiko na shekaru biyu saboda annobar Covid-19. To sai dai a bana ana iya cewar, abubuwa kalilan ne, kamfanonin Jamus da ma na sauran sassan duniya ke iya alfaharin gabatarwa, biyo bayan katse hanyoyin zirga zirga tsakanin kasashe saboda annobar. A yanzu haka babbar matsalar da ake fuskanta ita ce ta makamashi a sakamakon yakin da ke gudana a Ukraine. 

Samfurin kayayyakin masana'atuHoto: Dwi Anoraganingrum/Future Image/IMAGO

Wakilan kamfanoni 2,500 ne suka halarci bikin, don baje kolin kayayyakin da suka sarrafa a maimakon 5,000 da suka saba zuwa kafin barkewar annobar ta corona. "Sauyi a masana'antu" shi ne taken bikin na bana, da ke kira ga masana'antu da su zage damtse kada kuma su yi watsi da annobar da karuuwar farashin makamashi biyo bayan yakin kasar Ukraine.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz tare da Firaiministan Portugal Antonio Costa, su ne suka jagoranci bude bikin baje kolin na Hannover. Scholz ya godewa irin rawar da kamfanoni suka taka wajen bada goyon bayansu ga kakaba wa Rasha takunkumi, daura da farin cikin sake dawo da bikin.

Bikin ya gudana a birnin HannoverHoto: Dwi Anoraganingrum/Future Image/IMAGO

Yakin na Ukraine na bukatar martanin sauya alkibla domin shawo kan matsalar karanci da tashin farashin makamashi a sassan duniya. A baya bayan nan, an fara daukar matakai a zahiri kuma cikin gaggawa. A watan Mayu Kungiyar EU ta sanar da matakin zuba jari na wajen euro biliyan 300 domin tallafawa Turai daina dogaro da Rasha a bangaren makamashi.

A nan Jamus kuwa, an samu ci gaba inda masu mulki ke zama cikin shiri wajen taimakawa kalubalen da 'yan kasuwa ke fuskanta. A duniyar da muke ciki a yanzu, mahukunta na kara bayyana manufofinsu ta yadda za su tsarawa kamfanoni yadda za su tafiyar da kasuwancinsu. Wannan na faruwa cikin sauri, amma  kamfanonin na da iyakar aikin da za su iya yi. Duk da kalubalen da ake fuskanta a sassan duniya dai, a kwai bukatar hada karfi da karfe wajen ceto tattalin arzikin kasashe.

Mahalarta bukin baje kolin na birnin Hannover dai za su baje fasahu da kuma irin kayayyakin da kamfanonin ke sarrafawa, wanda ke zuwa shekaru biyu bayan barkewar annobar corona.