Amurka: Baki na ci gaba da fuskantar kalubale
June 4, 2026
Cikin wani sako da ya saki ta kafar sada zumunta, a dunkule shugaban na Amurka ya umarci bankuna su rufe asusun yin ajiya ko karbar kudi da duk wata harka a bankuna da mutanen da ke zama a kasar ba da izini ba suke yi. Babbar hujjar da Shugaba Donald Trump ya bayar ita ce, bude asusu a bankuna yana habaka aniyar ci gaba da shigowa ko zama Amurka ba da izini ba. Ya kara da cewa, harkar muggan kwayoyi da zambatar bankuna da kuma amfani da bankunan wajen boye tallafin jin-kai da gwamnati ke bayarwa.
Trump ya cika burinsa?
Fadar shugaban Amurkan ta White House ta yi karin bayani cewa, dokar za ta kuma rage hanyoyin karbar bashin da mutane marasa takardu suke ci daga karshe su ki biya musanman idan an fitar da su daga kasar. Trump ya dade yana yin kashedi, a kan irin matakan da zai dauka a kansu. Karkashin tanadin wannan doka mai sarkakkiya, daga yanzu gwamnati za ta fara kwato kudin tallafin da ake ba irin wadannan mutane da nufin mayar da su ga 'yan kasa ko masu izinin zama na halas da suke biyan haraji.
Wannann wata babbar guguwar canji ce da aka dade ba a taba ganin irin ta ba, ayar tambaya ita ce: Ta yaya bankuna za su iya bin diddigin irin wadanan masu hulda da su da suke amfana da su? Ita kan ta gwamnatin wadanne matakai za ta bi, ta tursasa yin aiki da wannan doka? Haka kuma, mutane nawa da mai yiwuwa ma 'yan kasa ne da suke yin ajiya a bankuna wannan doka za ta iya yin kuskure ta rutsa da su? Akwai yiwuwar ganin karuwar mutane marasa takardu da za su hanzarta rufe asusun ajiyarsu a bankuna.
Samun kudi ta barauniyar hanya
Haka kuma dokar, za ta iya yin illa wajen sa idanu da ake yi ga kofofin samu da hanyoyin kashe kudi da mutane marasa takardu suke da su. Dalili kuwa shi ne, kafin mutum ya bude asusu sai ya samu wata lambar zama a kasa da shi kadai yake da ita. Cikin ruwan sanyi, gwamnati za ta iya kanainaye hanyoyin shiga da fitar kudi. Amma wannan sabuwar doka da ta takura su, tamkar kasuwa ce aka bude ga barauniyar hanyar nema da kashe kudi ga mazauna Amurka ba da izini ba. Akwai yiwuwar Bankuna da wasu 'yan rajin kare hakkin baki su tafi kotu, domin takawa wannan sabuwar doka burki.
Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar