1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Bakin haure sun mutu a kokarin shiga Turai

Ramatu Garba Baba
February 18, 2023

Bakin haure akalla 18 aka tabbatar sun mutu a yayin da suka yi yunkurin shiga Turai ta barauniyar hanya daga kasar Bulgariya da ke yankin Balkan.

Bakin haure 18 sun mutu a kokarin shiga Turai
Bakin haure 18 sun mutu a kokarin shiga TuraiHoto: Georgi Paleykov/NurPhoto/IMAGO

Yan sanda a Bulgariya sun ce sun gano wata motar dakon kaya dauke da gawarwakin bakin haure kimanin goma sha takwas, ana ganin sun mutu ne saboda karancin iska da ya sa suka galabaita. Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta ce, jami'an sun gano motar a yashe a wata babbar hanya kusa da Sofiya babban birnin kasar. Bayanan farko da ta ce ta samu, ya nunar da cewa, motar na dauke da bakin haure kusan arba'in amma tuni aka kai wadanda aka gano na numfashi zuwa asibiti in da ake ba su kulawar gaggawa. 

Hukumomin ba su yi karin bayani kan asalin bakin hauren ba amma wasu kafofin yada labaran kasar ta Bulgariya sun ruwaito cewa dukkaninsu 'yan kasar Afghanistan ne da ake zargin masu safarar mutane ta barauniyar hanya ne suka yi kokarin shigo da su kasar da ke yankin Balkan.