Mutuwar bakin haure 20 a tekun Libiya
November 13, 2020Talla
Kungiyar ta ce hadarin ya faru ne a yankin Sorman mai tazarar kilomita 180 daga Arewa maso gabashin birnin Tripoli, to amma sai dai kungiyar ta ce tana ci gaba da kulawa da wasu mata ukun da suka stira daga nutsewar wadanda yanzu hakan ke cikin damuwa.
Masu aiko da rahotanni sun ce an ko a ranar Alhamis din nan an shimfide gawarwakin bakin haure 74 da aka tsamo daga gabar tekun, kana kuma wasu daga cikin gawarwakin na sanye da rigunan ceto, lamarin da ya kara tayar da hankalin wadanda suka tsira daga nutsewar.