1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Bakin haure 27 sun halaka a Tekun Tunusiya

January 2, 2025

Lamarin ya auku sakamakon kifewar kwale-kwale guda biyu makare da mutane 110 da ke kokarin shiga Turai ta barauniyar hanya daga gabar Tekun Tunusiya.

Bakin haure 27 sun halaka a Tekun Tunusiya
Bakin haure 27 sun halaka a Tekun TunusiyaHoto: Borja Suarez/REUTERS

Jami'an kare fararen hula a Tunusiya sun ba da rahoton tsamo gawarwakin bakin haure kimanin 27 sannan kuma sun yi nasarar ceto wadansu 87 dukanninsu 'yan kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara bayan kifewar kwale-kwalen da ke dauke da su a jiya Laraba a gabar Tekun kasar.

Karin bayani: Dubban 'yan Afirka sun mutu a teku a 2024

Shugaban hukumar Sfax ta Tunusiya ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa Lamarin ya auku ne a sakamakon kifewar kwale-kwalen guda biyu makare da mutane 110 da ke kokarin shiga Turai ta barauniyar hanya.

Bugu da kari in ji jami'in mai suna Zied Sdiri, daga cikin gawarwakin mutanen 27 da aka gano a gabar Tekun a Tsibirin Kerkennah da ke gabashin Tunusiya har da mata da kuma kananan yara.