1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTunusiya

An kama bakin haure dubu 70 a Tunisiya

Abdoulaye Mamane Amadou
December 9, 2023

Jami'an garabar tekun Tunisiya sun ce sun kama dubban bakin hauren da suka so tsallakawa ta tekun kasar da niyar zuwa Turai ta barauniyar hanya a wannan shekara.

Lampedusa | Italiya| Bakin Haure
Lampedusa | Italiya| Bakin HaureHoto: Alessandro Serrano/AFP/Getty Images

Hukumomi a Tunisiya sun ce a wannan shekarar adadin ya ninka har kusan sau biyu idan aka yi la'akari da wadanda suka kudri anniyar bi ta tekun kasar don shiga Turai a shekarar da tagabata.

Daman dai kasashen Libiya da Tunisiya ne ke kan gaba, daga jerin kasashen da bakin haure ke yi wa sammako da zummar keta ruwan tekun Mediteraniyan da zummar samun inagantacciyar rayuwa a Tuari ta barauniyar hanya.

Fiye da bakin haure dubu biyar ne aka tisa keyarsu zuwa iyakokin Aljeriya da Libiya daga Tusnisiya a tsakiyar wannan shekara, a kokarin da hukumomin kasar ke yi na dakile kwararar bakin haure.