1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bakin haure masu yawa sun mutu a teku

June 15, 2023

Akalla bakin haure 79 ne suka nitse a ruwayen kasar Girka, yayin da ake fargabar mutuwar karin wasu masu yawa a ibtila'in da ya faru a ranar Laraba.

Hoto: HELLENIC COAST GUARD/REUTERS

Masu gadin kan teku a Girka sun ce akwai daruruwan bakin hauren da suka bata, baya ga wadanda suka mutu kawo i yanzu a sabon hadarin ruwa da ak samu a kan teku.

Galibin mutanen da hadarin ya rutsa da su dai sun fito ne daga kasashe irin su Masar da Syria da Pakistan da Afghanistan sai kuma wasu daga cikin su da ke Falasdinawa.

Bayanai dai na nuna cewa akwai matukar yiwuwar adadin wadanda za su mutu ya karu.

Jirgin ruwan da ya shako mutane da kuma kaya fiye da kima, na dauke da mutane kimanin 750 wadanda ke neman shiga kasashen Turai ala kulli halin.

Kasashen na Turai dai na fama da turuwar mutane daga wasu kasashen Larabawa da ma wasu daga yankin Afirka bakar fata.