1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bakin haure na ci gaba da mutuwa kan hanyar zuwa Turai

Salissou IssaSeptember 17, 2014

Rikice-rikice na cikin gida da koma-bayan tattalin arziki suna ci gaba da haddasa kwararar yan gudun hijira daga kasashen Afirka da gabas ta tsakiyar zuwa nahiyar Turai

Symbolbild Flüchtlinge Mittelmeer Bootsflüchtlinge Migranten
Hoto: picture-alliance/dpa

Bakin haure daruruwa ne yawancinsu yan Afirka, a 'yan kwanakin nan suka rasa rayukansu, a yunkurin zuwa Turai ta kan tekun Bahar Rum, inda kamarin lamarin ya sa hukumar yan gudun hijira O I M kira ga mahukuntan kasashen Tunusiya da Libiya da su dauki matakan hana bakin hauren tasowa daga yankunansu don rage asarar rayukan da ake samu.

Mutuwar bakin hauren dake neman shiga Turai ta kan tekun Bahar Rum, zuwa tsibirin Lampedusa na Italiya ba bakon abu bane, sai dai dimbin rasa rayukan da ake samu a 'yan kwanakin nan, abu ne dake tada hankali sosai. Tashin hankali a kasar Libiya ya taimaka ainun wajan karuwar masu ratsa tekun zuwa Turai sabili da rashin tsaro. Kakakin hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wato OIM ya bayyana dalilan da ke sa bakin haure son zuwa Turai.

"Matsaloli da dama ne ke sa bakin hauren barin kasashensu don zuwa Turai, misalin yaki a Siriya da Sudan Ta Kudu da Iraki, ga wahalar abinda za a ci, ana hannu baka hannu kwarya. Wannan hali ke sa mutane barin kasshensu".

Wani malami da ya bukaci mu sakaya sunansa, da ya taba biyo wannan hanya ta ruwa zuwa tsibirin Lampedusa da yanzu haka kenan kasar Jamus ya fada mana yadda suka ratso tekun na Mediterane:

Matasa da dama daga kasashen Afirka na son zuwa Turai ko ta halin kaka sabili da wankin kwakwalwar da ake masu. Salisu Umaru wani dan Nijar dake nan Jamus ya fada mana tunanin matasan:

Bakin haure kan hanyar zuwa TuraiHoto: picture alliance / ROPI

"Ketarowa Turai ma ba hutawa bane, ta la'akari da rashin aikin yi, ga wulakanci kala-kala, wanda yace da za a sake, ko da wasa ba zai biyo wannan hanya ba mai hadari inda yayi kira ga matasa".

Karuwar bakin hauren, daga kasashen duniya na daga hankali ga kasashen Turai sai dai rashin magance matsalar daga tushe ke sa lamarin ci gaba.

"Karfafa tsaro kan tekun ba shi ne zai magance matsalar ba, dole a nemi tushenta,, kuma yake-yake da yunwa da rashin tsaro da shugabanci na gari a kasashen suna taimakawa wajen kwararar yan gudun hijira zuwa Turai".

Tun farkon wannan shekara ta 2014 kimanin bakin haure dubu ukku ne suka rasa rayukansu a yunkurin shiga Turai ta tekun na Bahar Rum ko ta tkun Bakar Maliya