1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Bakin haure na cikin ukuba a Libiya

Lateefa Mustapha Ja'afar SB
June 26, 2026

Jaridun Jamus sun mayar da hankali kan cin zarafin bakin haure a Libiya da sunan dakile kwararar masu hijira zuwa kasashen Turai, gami da rawar da 'yan Afirka ke takawa a wasan neman cin kofin kwallon kafa na duniya.

Libiya I Bakin haure
Bakin haure a LibiyaHoto: Hazem Ahmed/AP/picture alliance

Sharhin da jaridar die Tageszeitung ta rubuta mai taken: Azabtarwa ta hanyar fakewa da dakile kwararar bakin haure zuwa Turai, a karshe an yankewa jami'in tsaron Libiya da al'ummomin kasa da kasa ke nema ruwa a jallo hukunci a kasarsa. Sai dai masu suka, na bayyana hukuncin da rufa-rufa.

Jaridar ta ce: Wata kotu a birnin Tripoli ta yankewa tsohon shugaban sashen gudanarwa da tabbatar da tsaro na fannin shari'a a Hukumar 'Yan sandan kasar Osma Almasri hukunci. Kotun ta same shi da laifin take hakkin firsinoni, inda zai kwashe tsawon shekaru bakwai da watanni hudu a gidan kaso.

Halin da bakin haure ke ciki

Bakin haure a LibiyaHoto: Gene Medi/NurPhoto/picture alliance

A cewar die Tageszeitung Mai shigar da kara na Libiya ya tuhume shi da laifin azabtarwa da mugunta da kuma cin-mutumcin firsinoni a gidan kason Mitiga da ke Tripoli babban birnin kasar, tun daga shekara ta 2015.

Kotun Hukunta Masu aikata Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa da ke birnin The Hague na kasar Neatherlands, ta bayar da sammacin kamoshi a kan wannan laifi tun watan Janairun 2025.

Gasar neman cin kofin kwallon kafa ta duniya

Ita kuwa a nata sharhin Neue Zürcher Zeitung da ta rubuta mai taken: Magoyin baya gwarzon dan kishin kasa a duniya, wanda ke kwaikwayon firaministan da aka yi wa kisan gilla Patrice Lumumba. Dan kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, ya zamo gwarzon Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa na Duniya.

Mai goyon bayan Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwanko a matsayin Patrice LumumbaHoto: Natacha Pisarenko/AP Photo/dpa/picture alliance

Jaridar ta ce: Da wahala, ake samun magoyin bayan 'yan wasan kwallon kafa da ke tsayawa kyam. Abin da aka san magoya baya da shi shi ne, yin tsalle da sumbatar rigunansu da zarara an jiyo kyamara zuwa gare su. A wasu lokutan, magoya bayan wata kungiya kan yi fada da takwarorinsu da ke goyon bayan wata kungiyar dabam ko su yi ta jefa abubuwa a filin kwallo kamar kofuna da makamantansu. 

Neue Zürcher Zeitung ta ce: Michel Kuka Mboladinga ba ya yin ko guda cikin wadannan dabi'u, hasali ma a kullum yana tsayawa sanye da kaya masu launin kasarsa tare da daga hannunsana dama tamkar mai sarawa zuwa ga filin. Yana tsayawa kyam har tsawon mintuna 90, abin da ya yi ke nan a wasan da Kwango ta sha kashi a hannu Columbia da ci daya da nema.

Mai goyon bayan Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwanko a matsayin Patrice LumumbaHoto: Natacha Pisarenko/AP Photo/dpa/picture alliance

Ita ma dai mujallar Sportbild ta yi nata sharhin ne kan Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa na Duniyar, inda ta ce: Dan wasan da zai bugawa kungiyar Bayern nan gaba Saibari ya taimaki Maroko zuwa zagayen kwaf daya. Mai shekaru 25 a duniya, Ismael Saibari Ben El ya ci gaba da zama maciyin kwallo.

Mujallar ta Sportbild ta ce: Dan wasan da ke shirin komawa kungiyar Bayern Munich ta Jamus, ya sake zura kwallo a wasan da kasarsa Maroko ta lallasa Haiti ta ci hudu da biyu. Saibari ya tabbatar da cewa, ya zura kwallo a duk wasan da kasarsa ta buga.

Afirka ta Kudu ta tsallaka zuwa maki na gaba

A nata sharhin kan Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa na Duniyar kuwa, Welt online cewa tayi: Karon farko a matakin kwaf daya, Afirka ta Kudu na murnar kafa tarihi a Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa na Duniya. Ta ci kwallaye biyu kacal a zagayen farko na gasar, sai dai ta samu maki hudu. Bayan ta yi nasara a kan Koriya ta Kudu, Afirka ta Kudu ta samu damar shiga rukunin kwaf daya a karon farko a tarihinta.

Masu goyon bayan kasar Afirka ta KuduHoto: AP

Mujallar Welt online ta ce: Mai horas da 'yan wasan na Bafana Bafana Belgian Hugo Broos ya yi nasarar lashe wasansu na karshe a zagayen farko da suka yi da Koriya ta Kudu da ci daya da nema, hakan ya bata damar kammalawa a matsayin ta biyu a rukunin A da kwallaye biyu kacal.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ita ma dai kan Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa na Duniyar na 2026 da ke gudana a kasashen Amurka da Kanada da Mexico. A sharhinta mai taken: Rashin nutsuwar da za a iya kaucewa, Senigal ta shiga Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa na Duniya da matsalolin da ta janyowa kanta. Ta ce: A yanzu kasar, na fuskantar barazanar kunyata. 

Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce: Senegal ta yi rashin nasara a karo na biyu a jere a gasar, abin da ke barazanar kora ta gida tun ba a je ko ina ba. Mai horas da 'yan wasan Senegal din Pape Thiaw ya ce, ya yi wuri a ce sun yi rashin nasara a gasar. Sai dai a yanzu, sun shiga tsilla-tislla. Ba wai sun gaza yin nasara a wasansu na farko da na biyu ba ne saboda fafatawa da Faransa da Norway da dukansu suka shahara a kwallo, kawai dai sun gaza mayar da hankali ne a wasannin da suka buga.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani