1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Bakin haure na wahala a Tunisiya

May 28, 2024

Masu saka ido kan kare hakkin dan Adam sun ce hukumomin Tunisiya na korar ba bisa ka'ida ba, matakin da suka ce yana ta'azzara sakamakon ayyaukan masu safarar mutane da aikata laifuka.

Bakin hauren Afirka a Tunisiya
Bakin hauren Afirka a TunisiyaHoto: Yousef Murad/AP/picture alliance

Misa li ga Olive Groove, wani mafakan 'yan gudun hijira ne mai cike da hatsarin gaske. Akalla akwai 'yan kasashen Afirka da ke kudu Sahara 80,000 da ke jiran damar tsga teku zuwa Turai. Mamadou wanda ba sunansa na gaskiya ba saboda fargabar kame a Tuniya, ya fito daga Chadi, ya gaza cimma tsibirin Lampadusa na kasar Italiya, duk da taimakon masu safarar mutane, inda ya kwashe watanni uku cikin matsanancin talauci da wahala. Fargaba da tsoro shi ne abin kwana da tashi na bakin hauren da ke son bude ido a Turai. Mamadou yana tafiyar kasa na akalla nisan kilomita 240 a dungurmin jeji, shi ma yana fuskanci matsaloli da dama.

Karin Bayani: Tarayyar Turai za ta taimaki Lebanon

Bakin hauren Afirka a TunisiyaHoto: Hazem Turkia/AA/picture alliance

Lauren Seibert, mai bincike a hukumar kare hakkin dan Adam musamman kan 'yan gudun hijira da bakin haure, ya ce abin da Mamadou da sauran bakin haure suke gamuwa da su a Libiya shi ne na korar gama gari ko ma a ce jifar da mutane a dokar daji. Ba wani sabon al'amari ba ne duk da munanen cin zarafi da aka samu a lokacin wannan juji da korar da suka shafe shekaru da dama ana yi a Arewacin Afirka daga kasashe da dama.

Tun a shekarar 2023, kungiyar Tarta shiga kawance da kasashen  Masar da Maroko da Mauritania da kuma Tunisiya, yarjejeniyoyin da suka hada da kudade na musamman da ake son a yi amfani da su wajen dakile kwararar bakin haure zuwa Turai. Ga masu lura da al'amura da dama, abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a manufofin kaura a Tunisiya na da matukar damuwa, tun bayan da Tunisiya ta zama wurin da bakin haure daga sassa daban-daban na Afirka ke ficewa daga nahiyar Afirka da ke fatan shiga Turai.