Bakin haure sun salwanta a teku
May 10, 2019Talla
Sama da mutum 70 ne ke a jirgin na ruwa, inda aka tannatar da mutuwar uku sauran kuwa suka bace a cewar jami'an kasar Tunisiya da lamarin ya faru.
Ma'aikatar tsaron kasar ta Tunisiya ta ce ana can ana amfanin da dababru daban-daban, na ganin an tsamo gwamman mutanen da suka nitsen a ranar Juma'a.
Tekun Bahar Rum dai ya kasance wane wajen da ke lakume rayukan jama'a galibinsu Afirkawa, wadanda ke hankororn ketarawa kasashen Turai, ala kulli halin.