1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bam ya halakad da sojojin Amirka guda 4 a Iraqi.

May 18, 2006

Wani bam da aka ɗana a bakin titi, ya janyo mutuwar sojojin Amirka guda 4 yau kusa da birnin Bagadaza. Wani tafintansu, ɗan ƙasar Iraqin, shi ma ya baƙwancin lahira sakamakon tashin bam ɗin.

Asarar waɗannan sojojin guda 4 yau, da kuma wani sojan rundunar mayaƙan ruwan da ya mutu jiya a yammacin Iraqin, sun sa adadin sojojin Amirkan da aka kashe a Iraqin a cikin wannan watan kawai, ya tashi zuwa 51. Gaba ɗaya dai, a ƙalla sojojin Amirka dubu 2 da ɗari 4 da 54 ne suka mutu a Iraqin, tun shekara ta 2003, yayin da shugaba Bush ya ƙaddamad da yaƙi ƙasar don hamɓarad da gwamnatin Saddam Hussein.

A halin da ake ciki yanzu dai, Firamiyan Iraqin mai jiran gado, Nuri al-Maliki, yana nan yana ta yunƙurin rarraba madafan iko ga jami’an da jam’iyyun siyasa suka gabatar masa da sunannakinsu , kafin ya gabatar wa Majalisa gwamnatinsa ta haɗin kann ƙasar, wadda a ran asabar ne ake sa ran ’yan Majalisar za su ka da ƙuri’un amincewa da ita. Mahukuntan birnin Washington dai na kyautata zaton cewa, kafa gwamnatin, wadda za ta ƙunshi ’yan shi’a da ’yan Sunni da kuma Kurdawa, ita ce za ta kawo ƙarshen tashe-tashen hankullan da ake ta samu a ƙasar a halin yanzu.