Mutane hudu sun jikkata
January 7, 2021Talla
Wani abu mai fashewa ya tarwatse tare da hallaka sojojin Jamhuriyar Kamaru guda hudu da kuma wani farar hula guda, a yankin Ambazoniya na masu amfani da turancin Ingilishi.
Kimanin mutane uku ne aka samu rahoton cewa sun jikkata, wadanda kuma yanzu haka suna karbar magani a wani asibiti.
Mai magana da yawun rundunar sojin kasar Rene Emmanuel Sadi ya bayyana cewa abin ya rutsa da dakarun nasu ne, yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga wurin wani biki a yankin Mbengwi.
Wasu alkalumma sun bayyana cewa akalla sama mutane dubu uku ne suka rasa rayukansu, inda kuma wasu sama da dubu dari bakwai suka tsallake matsugunnansu tun bayan zafafa hare-haren da 'yan tawayen suka yi a shekara ta 2017.