Afganistan: Bam ya kashe mutane a taron addini
December 18, 2020Talla
Hukumomin gwamnatin Afganistan sun tabbatar da mutuwar fararen hula akalla 15, wasu da dama sun jikkata a sabon harin bam da mayaka suka tayar yayin da al'ummar musulmi ke taron karatun Al-Kur'ani.
Babu kungiyar da ta dau alhakin harin kawo yanzu, sai dai dama dakarun gwamnati da mayakan Tliban sun sha dauki ba dadi a lardin Ghazni. Kuma sabon harin yazo ne bayan wani kazamin harin kunar bakin wake da ya kashe jami'an tsaro 30. Duk dai wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnati ke shirin sasantawa da mayakan Taliban.