Bam ya tarwatsa motar tattara kuri'u a Afghanistan
April 6, 2014Bayanai daga yankin Kundunz na kasar Afghanistan, sun ce harin ya faru ne a daidai lokacin da wata babbar mota dauke da akwatunan kuri'un zaben da aka gudanar a wannan kasa ke ficewa, inda ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku da suka hada da matukin motar, da jami'in tsaro guda da kuma wakilin hukumar zaben jihar.
Motar dai da ke dauke da akwatuna guda takwas cike da kuri'un da aka kada, ta tarwatse ne yayin da akwatunan suka yi kaca-kaca da ma kuri'un dake cikin su. Hakan ta faru ne a kokarin da ake, na tattara sakamakon zaben a fadin kasar ta Afghanistan.
Shugaban hukumar zaben wannan yanki Amir Amza Ahmazai, ya tabbatar da wannan lamari, amma kuma yace kuri'un dama tuni an kidaya su kuma an sanar da sakamakon su kafin ma motar ta bar wurin..
Iri-irin wannan bam dai na galgajiya, na daga cikin ababan da 'yan Taliaban ke amfani da su wajan kai hare-haren su, tun bayan da aka kawar da su daga karagar mulkin kasar a shekarar 2001.
Kasar ta Afghanistan, da ke cikin kasashe matalauta, na da a kalla al'ummar da yawanta ya kai milian 28.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu