1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Bama-bamai a birnin Maiduguri na Najeriya

March 17, 2026

Harkokin rayuwa sun fara komawa a sassan birnin Maiduguri inda aka bude kasuwa domin jama'a su ci gaba da hada a lokacin da ake ci gaba da aikin jinkai na majinyata kusan dari biyu ke samun kulawar likitoci a asibitoci.

Hare-haren bama-bamai a birnin Maiduguri na Najeriya
Hare-haren bama-bamai a birnin Maiduguri na NajeriyaHoto: Jossy Ola/AP Photo/picture alliance

Bam na farko wanda ake ganin shi ne ya fi yin barna ya tashi da yammacin Litinin (16.03.2026) bayan Musulmi mabiya addinin Islama da ke azumin watan Ramadan sun bude baki a wani wuri na cikowar jama’a a bakin kasuwar 'Monday Market' da ke cikin kwaryar Maiduguri, fadar gwamnatin jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

Shaidun gani da ido

Hare-haren bama-bamai a birnin Maiduguri na NajeriyaHoto: AP Photo/dpa/picture alliance

A cewar Malam Adamu Manzo wani da abin ya faru a kusa da shi fashewar ta kunar bakin wake ne kuma ta yi muni saboda yadda ya ga aka yi jigilar kwashe gawawakin a wurin, inda ya tabbatar da ganin mutane 27 da suka mutu.

Bayan fashewar Bam na farko ne kuma aka sake jin wata fashewar a yankin 'Post Office' inda nan ma dai ake da cikowar jama’a kana na uku ya tashi a mashigar Asibitin Koyarwa na jami’ar Maiduguri.

A duk wuraren an samu mutuwar mutane da wasu da suka jikkata wanda yawanci aka kai su asibito mafi kusa da su domin samun kulawar likita ta gaggawa.

Hukumomi sun tabbatar da abin da ya faru

Hare-haren bama-bamai a birnin Maiduguri na NajeriyaHoto: AFP

Mazauna yankunan sun ce karar fashe-fashen sun jefa mutane cikin firgici, inda mutane da dama suka ruga zuwa gidajensu ko kuma neman mafaka domin tsira.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Borno, Mataimakin Sufurtandan 'yan Sanda Nahum Daso, ya tabbatar da hare-haren sai dai jami’ansu sun killace wuraren ana gudanar da bincike da kuma tabbatar da tsaron jama’a, yayin da ake ci gaba da tattara bayanai kan adadin wadanda abin ya shafa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani