1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaKamaru

Zumunci saboda dokar 'yan aware a Kamaru

October 17, 2023

Yayin da rikicin 'yan aware da ke neman ballewa daga Kamaru ke cika shekaru bakwai, wani abu da ya fi damun mazauna Bamenda shi ne kullen da 'yan bindigar ke yi musu a wasu ranakun mako.

Kamaru | Bamenda | Kisa | Zaman Gida | Doka | 'Yan Aware
'Yan jarida na cikin wadanda ke fuskantar kisan dauki dai-dai a KamaruHoto: Mbuh Stella/DW

A irin wannan yanayi da kasuwanni da makarantu gami da ma'aikatu ke garkame, wasu mazauna syankin Bamenda da 'yan awaren ke yi musu kulle sun yanke shawarar haduwa a wasu wurare na musamman da ba a fili ba domin rage wa kai takaici. A wani waje  da ake shakatawa cikinsa da ake kira mile two a Nkem cikin Bamenda duk da kasancewar tituna duk  fayau kowa na gida saboda hali na fargabar rashin tsaro, wata mashaya na budewa a ranakun Litinin din mako kawai, inda masu shiga ke zuwa debe wa juna kewa da rage kunci. Kafin ma a yarda a bai wa mutum abin da yake bukata, lallai ne sai ya nuna shaidar cewa mazuani ne shi a unguwar ko birnin saboda ba a maraba da bakuwar fuska.

Hari kan yara 'yan makaranta a Kamaru

03:28

This browser does not support the video element.

Wanda ya mallaki wannan waje da ya fi son kawai a kira shi da suna Spice Boy, ya ce yana cinikin da ya kai Euro 50-70 kwatankwacin abin da ya dan haura Naira dubu 50-70 a ranakun da ake kyale mutane su dan fita yayin kuma da yake samun ninkin hakan a ranakun da aka hana fita. Baya ga mahada ta cikin unguwa da ake samu a Bamenda ga masu kwankwadar barasa, akwai ma wasu da ke haduwa ta zumunci  tsakanin abokai da ba mashaya ba. Akwai kungiyar da ake kira da "ka san makwabcinka" da ke ta taimakon juna da kuma ta masu harkokin wasanni. Ranakun Litinin ne kowa ke gida karkashin dokar zamaan tilas ta 'yan awaren, kuma a ranar mazauna yankin ke zuwa taro da suka yi wa lakabi da Njangi. A gidajen tarukan na Njangi dai, akan tara kudin adashi wanda ake kwashewa tsakanin mambobi.