Ban da Brahimi sun yi wa bangarorin da ke cikin rikicin Siriya tayin shiga tsakaninsu
March 3, 2013Talla
Bayan wani zama da suka yi kusa da yankin Lusanne na kaasr Switzerland, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya(MDD) Ban Ki Moon, da manzon kasa da kasa na musamman a Siriya, Lakhdar Ibrahimi sun ce Majalisar Dinkin Duniya za ta yi madallah da duk wata tattanawar da za a shirya tsakanin wani wakili mai karfi daga bangaren 'yan adawa da kuma wata karfaffar tawwaga ta gwamnatin Siriya. Ita dai MDD ta kuduri niyyar taimaka ma wannan tattaunawar. A cikin jawabinsu na hadin-gwiwa bayan ganawar tasu Ban da Brahimi sun ce sun tattauna akan kalaman da aka jyo a baya-bayan nan daga bakin 'yan adawa da kuma gwamnati da ke bayyana niyarsu ta shiga tattaunawa.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu