Ban Ki-Moon ya yi kira ga Isra'la
September 17, 2010Talla
Sakataren Majalisar Ban ki-Moon shi ya bukaci kasar Isra'ila da ta dakatar da shirinta na gine ginen a wuraran share wuri zauna da ke yamma da gaɓar kogin jordan a daidai lokacin da wa'adin da aka kayyade ke kammala a karshen wannan wata.
Mista Ban ki Monn ya ce mun jadada kudirin Majalisar Ɗinkin Duniya na ƙasa da ƙasa akan Isara'ila wanda ya haramta ci-gaba da yin gine gine a yankunan da Palasdiniyawa suka mallaka.
Fraministan dai na Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dage akan bakansane cewa babu gudu babu ja da baya akan shirin
a ƙarshen taron da aka kamala tsakanin shugabannin yankin na gabas ta tsakiya tare da hallarta sakatariyar harkokin waje Amurka .
Mawallafi :Abdurahaman Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar