1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki Moon ya yi taron manema labarai na farko a wannan shekara ta 2008

January 8, 2008

Majalisar Ɗinkin Duniya zata mayar da hankali wajen yaƙi da talauci a duniya

Ban Ki MoonHoto: AP

Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya(MƊD) Ban Ki Moon ya yi kira da a mayar da shekara ta 2008 ta zama shekara ta nuna zumunci ga mafi yawan mutanen da ke fama da matsalolin talauci a duniya. A saboda haka ayyukan raya ƙasa zasu kasance jigo a muhimman batutuwan da MƊD zata mayar da hankalin kansu a wannan shekara, inji sakatare janar ban Ki Moon.

Ban

Ya ce “A cikin watan satumba zamu gudanar da wani taro na shugabannin ƙasashen duniya a babbar mashawartar MƊD. A gun wannan taro za mu sake karfafa manufofin mu na cimma burin nan na raya kasashe wato Millenium Development Goals. Zamu fi mayar da hankali musamman a kan wadanda suka fi fama da matsalolin talauci.”

Tun a gun taron ƙoli kan sauyin yanayi da ya gudana a ƙarshen shekarar da ta gabata aka fara ganin wannan alama. An ɓullo da wani shiri dangane da sauyin yanayi, wanda za a yi amfani da shi da nufin ƙarfafa yaƙin da duniya ke yi da ɗumamar doron ƙasa tare da samar da wata yarjejeniya wadda zata maye gurbin yarjejeniyar birnin Kyoto.

Ban:

Ya ce “Hanyar da za´a bi bayan taron birnin Bali zata kasance mai wahala. Shekaru biyu ba zasu isa a samar da wata yarjejeniya wadda zata samu amincewar dukkan ƙasashen duniya ba. Buri na shi ne a ci-gaba da marawa wannan matsayin da muka kai baya.”

Ban ki Moon ya nuna damuwa musamman dangane da halin da ake ciki a ƙasashen Afirka kamar Sudan, Kenya da kuma Chadi. Saboda haka ya yi kira da a yi ƙokarin cimma wani sakamako a tattaunawar samar da zaman lafiya a yankin Darfur, don kawo ƙarshen rikicin wannan lardi dake yammacin ƙasar Sudan. To sai dai ba wani ƙarin bayani dangane da wani ƙarin angizo a sauran yankunan da ake fama da rikici a cikin su. Wato kenan shekara ɗaya bayan ya dare kan kujerar babban sakataren MƊD Ban Ki Moon bai sanya wani dogon buri ba in ban da bin manufofin majalisar. Ban ɗan ƙasar Koriya Ta Kudu ya gamsu da aikin sa to amma ´yan jarida da suka halarci taron manema labaru sun yi ƙorafin cewa a bara an fuskanci tafiyar hawainiya wajen aiwatar da ayyukan majalisar.

Ban:

“Ba na son yin magana game da nasarori. Amma a shekarar da ta wuce na ɗauki matakan ganin an samu ci-gaba a batutuwa da dama.”

Ayyukan dake gaban MƊD ba kaɗan ba ne, musamman tashe tashen hankulan kasar Kenya da Sri Lanka a farkon wannan shekara sun nunar a fili cewa da akwai jan aiki gaba.