1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki Moon ya ziyarci Niger

November 6, 2013

Wakilan Majalisar Dinkin Duniya ta kai wata ziyarar aiki ta yini daya a kasar Niger karkashin jagorancin sakatare janar na majalisar Ban Ki Moon domin tattauna batun tsaro da raya kasa.

Hoto: picture alliance/abaca

Tawagar Majalisar Dinkin Duniyar dai ta tattauna da hukumomin kasar Niger akan sabon tsarin ci gaban yankin kasashen sahel wanda Majalisar Dinkin Duniyar ta girka tun a shekara ta 2012 da kuma ta ke son soma aiwatar da shi nan ba da jimawa ba. Ko baya ga maganar tsaro da tattalin arziki Niger din ta samu tallafin kudi na sama da Euro miliyan 180.

Tawagar Majalisar Dinkin Duniyar ta iso ne a kasar ta Niger a ci gaba
da rangadin da ta soma a cikin kasashe biyar na Sahel domin tattaunawa
da hukumomin kasar Niger dan jin ra'ayinsu dangane da tsarin
majalissar dinkin duniya na ci gaban yankin sahel, da ke maida hankali
a kan fannoni ukku, wadanda su ka hada da tafiyar da shugabanci na
gari da maganar tsaro da samar da zaman lafiya da kuma kyautata jin
dadin alumma. Majalisar Dinkin Duniyar ta fito da wanann tsari ne ga
yankin na Sahel wanda ke fama da matsaloli na tsaro da a yau aka gano
cewa na da nasaba ne da matsalar talauci da jahilci da ya dabaibaye
al'ummomin kasashen yankin, kamar dai yadda sakatare janar na
Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya ambato a cikin jawabinsa.

"Ya ce mun samu cikakken darasi na rayuwa da ya nunar da cewa zaman
lafiya ba ya samuwa matsawar babu ci gaba, haka zalika zancan ci gaba
bai taso ba matswar babu zaman lafiya. Kenan ya zamo dole zaman lafiya
da ci gaba su yi tafiya kafa da kafada. Akan haka ne wanann tsari namu
na yankin Sahel ya tanadi hada kai guri daya tsakanin hukumomin
Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatocin kasashe dama kuma kungiyoyin
yankuna daban daban."

Da ya ke mayar da martani dangane da wanann tsari na Majalisar
Dinkin Duniya kan batun ci gaban kasashen Sahel shugaban kasar Niger
Mahammadu Isufu bayyana gamsuwarsa ya yi yana mai cewa:

Tsarin da Majalisar Dinkin Duniyar ta fito da shi tsari ne da
ya yi daidai da iirin namu tunani da mu ka yi na hanyoyin da ya
kamata a bi domin bunkasa tattalin arzikin kasarmu dama sauran
kasashemmu na Sahel dama kalubalantar matsalolin tsaron da su ke
fusknata. Don haka a yau lalle Niger na sa ran samun wani abu daga
wanann shiri na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya yi daidai da wasu
gurirrika da mu ka sa a gaba, kamar su shirin 3N na 'yan Niger su ci da
'yan Niger, ko na neman rage yawan yaduwar al'ummarta, dama abun da ya
shafi kiwon lafiya, ilimi da samar da ruwan sha ga alumma.

Matsalar yunwa a kasar NigerHoto: picture-alliance/dpa


Saidai ko baya ga wadannan jawabai, za a iya cewa kolliya ta biya kudin
sabulu, inda daga karshe Kungiyar Tarayyar Turai ta tallafawa Niger da
kudi sama da Euro miliyon 181, kwatankwacin miliyan dubu 120 na Cefa
domin gudanar da wasu ayyuka da su ka hada da gina hanyoyi da
tallafawa kananan hukumomi a fannin kiwon lafiya da ilimi da ma tsaro,
musamman a cikin jihohin yankin arewacin kasar. A karshe bayan kasar
Niger tawagar ta tashi zuwa kasar Burkina Faso.

Pirayim Ministan Niger Brigi RafiniHoto: Getty Images