1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki-moon zai ziyarci ƙasar Iran

Usman ShehuAugust 22, 2012

Ban Ki-moon ya yi watsi da adawar Amirka da Isra'ila kan ziyarsa izuwa ƙasar Iran, inda ya tabbatar da kai ziyarar a makwan gobe

Der iranische Staatspräsident Mahmud Ahmadinedschad hat bei einem Treffen mit dem UN-Generalsekretär Ban Ki Moon die Notwendigkeit bekräftigt, zur Verteidigung der Rechte aller Völker die Struktur der UNO zu reformieren. Zulieferer: Ali Akbar Ghanbari Bildbescheibung: Ahmadinejad tift Ban Ki Moon Lizenz: Frei Quelle: www.dolat.ir Eingestellt am 20.09.2010
Mahmud Ahmadinejad da Ban Ki Moon a birnin New YorkHoto: dolat.ir

Sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban ki-Moon zai hallarci taron ƙungiyar ƙasashen yan ba ruwammu da zai gudana a ƙasar Iran, wanda zai a buɗe a mako mai zuwa. Inda ya yi watsi da kiran da Amirka da Isra'ila suka yi masa na ya ƙauracewa taron tunda dai a ƙasar Iran ake yinsa. Kakakin Sakatare janar din ya shaidawa manema labarai cewa, za mu mutunta ƙasar Jamhuriyar Islama ta Iran, inda Ban ki-moon zai yi amfani da ziyar ta sa domin nuna wa mahukunta Tehran irin fatan da ƙasashen duniya ke son gani a gare su. Kamar yadda kakakin na sa ya bayyana, wasu daga batutwan da Ban ki-moon zai tattauna da mahukunta Iran, sun hada da shirin nukiliyar ƙasar da yaƙi da ta'addanci da kare yancin bil'Adama, kazalika da batun rikicin ƙasar Siriya. Don haka Ban Ki-moon zai kasance a ƙasar ta Iran na tsawon kwanki uku.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu

RTR