Zambiya: Mutuwar jagoran kwatar 'yanci
June 18, 2021Tsohon shugaban kasar na Zambiya wanda ya yi gwagwarmayar samun 'yancin kasar da ake wa lakabi da sunan uban kasa, wato Kenneth Kaunda ya rasu a jiya a wani asibiti a Zambiya yana da shekaru 97 bayan da ya sha fama da lalurar ciwon limoniya(Pneumonie). Kenneth David Kaunda na zaman guda daga tsofaffin shugabannin Afirka wadanda ake mutuntawa kana ana ganinsa da kima, duk da cewar a tsawon mulkinsa na shekaru 27 al'ummar kasarsa ta Zambiya sun wahala. An haifi Kaunda a ranar 28 ga watan Afrilun shekara ta 1924 tsakanin tsohuwar Rhodesia ta Arewa da Kwango a garin Lubwa. Iyayensa sun zo ne daga Malawi maihafinsa limamin coci ne.
Karin Bayani: Zanga-zangar adawa da sakamakon zabe
Ya kasance mallamin makaranta a karkashi mulkin Turawan mulkin mallaka na Birtaniya. Sai dai tun lokacin ya yi ta kutsawa cikin harkokin siyasa, abin da yasa ya yi ta shan dauri a gidan kurku. Jama'ar Zambiya za su dade suna tunawa da shi: ''Ya yi abubuwa da yawa ga kasa har ma da gabashin Afirka baki daya. Ya taimaki kasashen Namibia da Angola da Mozambik da Zimbabuwe da ke makabtaka, wajen samun 'yancin kai."
Ya dai taka muhimmiyar rawa wajen warware rigingimu a nahiyar Afrika musamman a Afrika ta Kudu, lokacin mulkin wariyare launin fata.Tun da ya yi ritaya a shekara ta 2000, Kenneth Kaunda ya rika shiga tsakani a rikice- rikicen da aka yi ta fama da su a Kenya da Zimbabuwe da Togo da Burundi. Ya kasance dan fafufukar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDs ko kuma SIDA, bayan da guda daga cikin 'ya'yansa ya mutu sakmakon cutar.
Karin Bayani:Kalubale gabanin zaben Zambiya
Sai dai daga bisani mulkinsa ya kasance mai tsauri kamar na Kwame Nkurmah da Julis Nyerere tare da yunkurin batar da duk wani wanda zai nuna masa adawa a tafiyar gwamnatinsa, a cewar Friedrich Stenger wani mai yin fashin baki a kan al'amura: "Kenneth Kaunda dan siyasa ne da ya san duk abin da ya kamata ya yi. Ya dage a kan matsayinsa kuma ya san yadda ake rabuwa da miyagun mutane."
Shugaba mai ci na Zambiya Edgar Lungu ya bayyana alhininsa, na rashin mutumin da ya kira gwarzo wanda ya gina Zambiya.