Banayi kan rikicin kyamar baki a Afirka ta Kudu
June 3, 2015Farfesa Abdullahi ashafa malami a Jami'ar Jihar Kaduna ta Najeriya ya yi mana bayani kan abin da ke janyo rikicin a kasar Afirka ta Kudu da ake kai hare-hare kan 'yan kasashe ketere. Malamin ya nunar da cewa 'yan Afirka ta Kudu sun dade karkashin mulkin nuna wariyar launin fata lokacin mulkin Turawa tsiraru. Kuma bayan kawar da gwamnatin nuna wariyar Shugaba Nelson Mandela ya fito da mulkin hadin kan kasa, amma bakeken fata tun daga lokacin suka fara nuna wa bakin bakake wariya. Yayin da sauran bakake suke ganin sun taimaka wajen samar da 'yanci ga 'yan kasar.
Malamin ya kara da cewa dalilin tattalin arziki na kan gaba saboda galibi baki suna aiki, yayin da marasa aiki 'yan kasar ke gani an kwace musu guraben ayyuka. Daga karshe malamin ya nemi gwamnatin AFirka ta Kudu ta tashi tsaye wajen samar wa matasa da aiki.