1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaBangladesh

Firaministar Bangladesh ta ajiye mukaminta

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 5, 2024

Dubban al'ummar Bangladesh sun barke da tsallen murna da shewa da raye-raye, bayan Firaminista Sheikh Hasina ta sanar da ajiye mukaminta tare da barin kasar zuwa makwabciyarsu Indiya.

Bangladesh | Sheikh Hasina | Murabus | Indiya | Zanga-Zanga
Tshohuwar firaministar Bangladesh Sheikh HasinaHoto: Peerapon Boonyakiat/SOPA Images/IMAGO

Gidan talabijin din kasar ta Bangladesh na Channel 24 ya nuna yadda masu zanga-zangar dauke da tutoci suka kutsa gidan tsohuwar firaministar, yayin da wasu fusatattu suka tumbuke mutummutumin mahaifinta Sheikh Mujibur Rahman da ke zaman gwarzon kwato 'yancin kasar da kuma dasa kamarori a lokacin da suke satar kayayyaki. Jim kadan bayan murabus din nata babban hafsan hafsoshin kasar Janar Waker-Uz-Zaman ya yi jawabi ga al'umma a gidan talabijin din kasar, inda ya tabbatar da cewa za su kafa gwamnatin rikon kwarya a Bangladesh. Firaminista Sheikh Hasina ta ajiye mukaminta da ta kwashe tsawon shekaru 15 a kai, bayan zanga-zangar makonni da al'ummar kasar suka kwashe suna yi. Da fari dai ta so murkushe zanga-zangar da dalibai suka fara tun farkon watan Yulin da ya gabata, sai dai bayan mummunar zanga-zanga a Lahadin karshen mako da ta halaka kimanin mutane 100 ta yar da kwallon mangwaro ta huta da kuda.