1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Jam'iyyar BNP ta yi ikirarin lashe zaben Bangladesh

February 13, 2026

Amurka da wasu manyan kasashe sun taya Tarique Rahman murnar nasarar da BNP ta yi a zaben 'yan majalisar Bangladesh, yayin da jam'iyyar hamayya ta masu kishin Islama ta yi watsi da shan kaye.

Bangladesch Dhaka 2026 | Tarique Rahman nach Stimmabgabe bei der Nationalwahl
Hoto: Md abu sufian jewel/NurPhoto/picture alliance

Jam'iyyar masu ra'ayin kishin kasa ta Bangladesh ta yi ikirarin samun nasara da gagarumin rinjaye a zaben 'yan majalisar dokokin kasar na farko da aka gudanar tun bayan boren da ya kifar da gwamnatin Sheikh Hasina a 2024.

Ko da shi ke har kawo yanzu hukumar zaben Bangladesh ba ta fitar da sakamakon zaben a hukumance ba, amma a cikin wata sanarwa jam'iyyar hamayya ta masu kishin Islmala ta yi watsi da shan kaye.

Sai dai bisa hasashen da gidajen talabijin na kasar suka bayar a safiyar nan ta Juma'a, jam'iyyar ta BNP na iya samu kujeru 212 daga cikin kujeru 300 na majalisar, abin da ya zarta kashi biyu bisa uku idan aka kwatanta da kujeru 74 na kawancen Jamaat-e-Islami.

Tuni dai Amurka da Pakistan da Indiya suka taya shugaban jam'iyyar BNP Tarique Rahman wanda ya shafe shekaru 17 yana gudun hijira a Landan murnar yin nasara a zaben 'yan majalisar na Bangladesh da ta kasance wani bangare na Pakistan kafin samun 'yancin kai a shekarar 1971.