Bangladesh: Sojin Myanmar sun dasa nakiyoyi a iyakoki
September 9, 2017![Bildergalerie Myanmar Rohingya Flüchtlinge flüchten nach Bangladesch](https://static.dw.com/image/40278417_800.webp)
Kasar Bangladesh ta ce sojojin Myanmar sun dasa nakiyoyi a kan iyakoki a tsakanin kasashen biyu yayin da musulmi yan kabilar Rohingya ke ci-gaba da yin kaura daga Myanmar zuwa Bangladesh. Sai dai sojojin sun musanta zargin.
A waje guda kungiyar kare hakkin bil Adama ta duniya Amnesty International ta ce ta sami hujjoji kwarara da suka tabbatar da cewa sojojin Myanmar sun dasa nakiyoyi akan iyakokin.
A halin da ake ciki kuma an fara baiyana damuwa kan karancin muhimman kayayyakin bukatu da kuma barazanar barkewar cutattuka a sansanonin yan gudun hijirar na Rohingya.
Rahotanni sun ce an fara samun kokawa kan abinci da ruwan sha yayin da mata da kananan yara ke bin motoci da masu tafiya a kasa suna barar domin samun abin da za su ci.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce musulmi yan Rohingya kimanin dubu 290 suka tsallaka zuwa Bangladesh a cikin makonni biyu da suka wuce.