1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaBangladesh

Sheik Hasina na shirin fuskantar hukunci

Abdourahamane Hassane
December 23, 2024

Kasar Bangladesh ta bukaci Indiya da ta mika mata tsohuwar firaministan kasar Sheikh Hasina domin a yi mata shari'a, duk da cewa ta samu mafaka a kasar.

Hoto: Government of Bangladesh

 Sheik Hasina, wacce ta mulki Bangladesh da sandar karfe, wadda gwamnatinta ta rika samun goyon bayan New Delhi, ta arce zuwa Indiya da jirgin sama mai saukar ungulu a ranar biyar ga watan Agusta lokacin da masu zanga-zangar suka mamaye fadar firayim minista a Dhaka, bayan shafe makonni suna yin borai. A tsawon shekaru 15 na mulki ana zarginta da keta hakin dan Adam tare da kulle jamaa da dama a gidan yari da yin kisa barkatai kan yan  adawa.